An sayar da zanen da wani dan Nigeria ya yi kan £1.2m

A baya bayan nan dai kasashen duniya na nuna sha'awar zane-zanen da a ke yi a Najeriya Hakkin mallakar hoto BONHAMS
Image caption A baya bayan nan dai kasashen duniya na nuna sha'awar zane-zanen da a ke yi a Najeriya

An sayar da wani zane a kan kudi sama da dala miliyan daya da rabi wanda daya daga cikin kwararrun masu zanen zamani a Najeriya ya yi wanda kuma shekaru kusan arba'in ke nan da bacewarsa.

Ben Enwonwu ne ya yi zanen na wata Gimbiya, da a ke kira Tutu a kudancin Najeriya a shekara alif dari tara da saba'in da hudu.

Rabon da a ga zanen dai tun a shekarar 1974 a lokacin da aka nuna shi a Legas, sai kwanan nan da aka gano shi a wani gida a arewacin Landan.

A baya-bayan nan dai, kasashen duniya na nuna sha'awar zane-zanen da ake yi a Najeriya kuma darajarsu ta karu.

Ben Okri wanda marubucin litafi ne da ya taba kashe gasar rubuta littafi ta Booker ya bayanna zanen a matsayin wani muhimin abu da aka gano a fasahar zane-zanen Afirka a cikin shekaru 50 da suka gabata.

Ya kuma ce wannan abun farin-ciki ne .

Mista Enwonwu ya yi zane-zane guda uku na gimbiya Tutu, sai dai dukkaninsu sun bata a shekarar 1994 bayan mutuwarsa.

Labarai masu alaka