Wa'adin dawo da kudade da ke ajiye a wajen Zimbabwe ya cika

Wa'adin dai an yi wa 'yan siyasa ne da 'yan kasuwa. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wa'adin dai an yi wa 'yan siyasa ne da 'yan kasuwa.

A Zimbabwe, wa'adin dawo da wasu kudade da ake ajiye da su a wajen kasar ya cika.

A kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa da kuma kawo karshen rashin kudi, Shugaba Emerson Mnangagwa ya baiwa jama'a wa'adin watanni uku su dawo da kudadensu Zimbabwe domin kaucewa hukuncin laifin ajiyar kudin mai tsauri.

Wa'adin dai an yi wa 'yan siyasa ne da 'yan kasuwa.

Sai dai yayin da shugaban ya ke cewa mutane da yawa sun bi dokar, jama'ar Zimbabwe sun kosa su san wadanda su ka karya dokar.

Hukumomi sun ce a yanzu da wa'adin ya cika, za a fara yin kame.

Labarai masu alaka