Dapchi: Gwamnonin jihohin arewa za su kara tsaro a makarantun kwana

Gwamnonin sun ce za su ci gaba da daukar matakai don ganin an kaucewa sake afkuwar sace daliban makarantu a nan gaba

Asalin hoton, STATE HOUSE

Bayanan hoto,

Gwamnonin sun ce za su ci gaba da daukar matakai don ganin an kaucewa sake afkuwar sace daliban makarantu a nan gaba

Kungiyar gwamnonin jihohin arewacin Nigeria ta amince da daukar matakai na sanya na'urorin daukar hoto na tsaro musamman a makarantun kwana na 'yan mata a jihohinsu.

Gwamnonin sun sanar da haka ne a karshen wani taro da suka kammala ranar Alhamis a Kaduna.

A cewar su, wannan na daga cikin matakan da su ke shirin dauka don samar da tsaro a makarantun kwana da ke jihohin.

Kungiyar gwamnonin ta kuma jajantawa al'ummar jihar Yobe game da sace daliban makarantar mata a Dapchi da mayakan Boko Haram suka yi.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya shaida wa BBC cewa suna goyon bayan matakan da gwamnati tarayya ke dauka na ganin an ceto daliban daga mayakan Boko Haram.

Kungiyar gwamnonin ta ce za ta ci gaba da daukar matakai don ganin an kaucewa sake afkuwar sace daliban makarantu a nan gaba.