Kasuwannin hannayen jari sun fadi saboda sabon tsarin harajin Amurka

Amurka na dogara da sama da kasashen Asiya dari wajen shigo da karafa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Amurka na dogara da sama da kasashen Asiya dari wajen shigo da karafa

Kasuwannin hannayen jari a gabashin Asiya sun fadi tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirinsa na kara haraji a kan gorar ruwa da karafa.

Hakan ya ruruta tsoron yiwuwar rudun cinikayya a fadin duniya.

Alkalluman Nikkei na kasar Japan sun sauka da kusan kashi uku cikin dari inda hakan ya fi shafar hannun jarin masu sarrafa karafa a Asiya.

Shugaba Trump dai ya ce zai sa hannu a kan karin harajin kashi ashirin da biyar cikin dari a kan karafa da kuma kashi goma cikin dari a kan gorar ruwa.

Kasuwar Hannayen jarin Amurka ta fadi

Komai ya tsaya cak a gwamnatin Amurka kan kasafin kudi

Labarai masu alaka