An ci tarar Man City kan wasanta da Wigan

Man City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sergio Aguero ya tsallake hukunci bayan an nuna ya turi wani dan kallo

An ci tarar Manchester City fan dubu hamsin kan laifin rashin tausar da 'yan wasanta a wasan da Wigan ta fitar da ita a gasar FA.

Man City ta amsa laifinta na rashin janyo hankalin 'yan wasanta a karawar ta zagaye na biyar da aka yi waje da ita.

'Yan wasan City da dama ne dai suka dabaibaiye alkalin wasa Anthony Taylor bayan ya ba Fabian Delph jan kati.

Korar Delph daga filin wasan da aka fafata a ranar 19 ga Fabrairu ya janyo muhawara tsakanin kocin City Pep Guardiola da abokin hamayyarsa Paul Cook.

Hukumar FA ta caji kungiyoyin biyu bayan kamala wasan, kuma ga alama babu wani dan wasa da hukunci zai shafa.

Labarai masu alaka