Ibrahimovic zai bar Man Utd- Mourinho

Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ibrahimovic yana kasarsa Sweden ta kira shi zuwa Rasha

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce akwai yiyuwar Zalatan Ibrahimovic zai bar kulub din a karshen kaka.

Ibrahimovic mai shekaru 36 wanda ya sabunta kwangilarsa ta shekaru daya a watan Agusta, bai dade da ya dawo taka leda ba, bayan ya shafe makwanni yana jinya.

Wasanni bakwai kawai ya buga wa Manchester United tun dawowarsa daga jinya a watan Nuwamba.

Kuma rabonsa da ya buga wasa tun lokacin da Burnley ta rike United a gasar Premier a washegarin kirsimeti.

Mourinho ya ce suna tunanin dan wasan na Sweden wannan ce kakarsa ta karshe a Manchester United.

Ibrahimovic, da United ta karbo daga Paris St-Germain a watan Yulin 2016, ya ci wa Kulub din kwallaye 28 a dukkanin wasanni 46 da ya buga a kakar da ta gabata.

Mourinho ya ce dan wasan na da 'yancin zabawa kansa makoma. Kuma kocin na Manchester ya ce ya daina saka dan wasan ne saboda a ganinsa har yanzu bai ida murmure wa.

Ibrahimovic ya buga kwallo a manyan kulub tun daga Ajax zuwa Juventus da Barcelona da AC Milan da Inter Milan da PSG kafin ya dawo Manchester United.

Labarai masu alaka