Masar: An kama wata mace bayan rahoton BBC

Mahaifiyar Zubaida
Image caption Mahaifiyar Zubaida ta ce ta na nan kan bakar ta, kan labarin da BBC ta wallafa na azbtarwa da batan 'yar ta watanni 9 da suka gabata

Hukumomin kasar Masar sun cafke wata mata 'yar asalin kasar da ta yi hira da BBC a kwanakin baya, inda gwamnati ta zarge ta da yada labaran karya.

A makon da ya gabata ne wani rahoto da BBC ta yi ya karade shafukan sada zumunta, inda matar ta bayyana yadda jami'an tsaro suka azabtar da ita da kuma 'yar ta mai suna Zubaida a lokacin da ake tsare da su.

Daga bisani bayan an sako su 'yar ta kara bata babu wanda ya san inda ta ke tun watan Afirilun shekarar da ta gabata.

Sai dai wani abin ban mamaki shi ne, a ranar litinin din da ta gabata kawai sai Zubaida ta bayyana a wani shiri da ake yadawa a gidajen talabijin din kasar, ta kuma bayyana ita sam babu wanda ya kama ta ko tsare ta bare kuma batun azabtar da ita.

Hukumomin Masar sun tsare ta na kwanaki 15 ana mata tambayoyi.

Hukumomin kasar dai sun ce dole BBC ta nemi afuwar al'uma da gwamnatin Masar kan rahoton da ta kira karya tsagwaronta.

A nata bangaren BBC ta ce ta amince da hanyoyin da ma'aikatanta suka bi dan tattara bayanan da rahoton ya kunsa, amma duk da haka za su tattauna da hukumomin Masar kan batun.

Jaridar Al-Ahram ta kasar ta rawaito cewa gwaamnati na zargin mahaifiyar Zubaida da yada labarin da ka iya jabyowa kasar zubewar kima a idon duniya, da kuma zargin ta na cikin wata kungiya da ke son ganin bayan gwamnati, amma ba a bayyana sunan kungiyar ba.

A ranar talata mahaifiyar Zubaida ta shaidawa gidan talabijin mallakar kungiyar 'yan uwa musulmi da ofishin ta ya ke kasar Turkiyya, cewa an tilastawa 'yar ta yin wadannan kalamai da ta yi na musanta ukuba da azabar da suka sha a hannun jami'an tsaron Masar.

Ta kara da cewa ta na nan kan bakar ta, na bayanin da ta yi wa BBC, ta musanta alaka da duk wata kungiya da ke fafutukar kawo karshen gwamnatin Masar.

A bangare guda kuma shugaba Abdul Fatta al-Sisi ya ce, cin mutuncin jami'an tsaro da fadar labaran karya akan su cin amanar kasa ne.

Labarai masu alaka