Ghana: 'Za mu tabbatar da tsaftar muhalli a Accra'

Nana Akufo Addo
Image caption Shugaba Nana Akufo Addo ya sha alwashin tsaftace birnin Accra

Shugaban kasa Nana Akufo Adoo yaci alwashin rage matsalar tsabtar muhalli daga Accra babban birnin kasar Ghana, inda yake da yawan mutane miliyan biyu.

Rashin tsabtar muhalli na yawan kawo matsalar ambaliyar ruwa da barkewar cututtuka kamar su amai da gudawa.

Baya ga cutar amai da gudawa, zazzabin cizon sauro ba ta babbar barazana ce ga al'umar da ke zaune a inda lamarin ya fi kamari.

Tarin bolar da ake jibgewa a kusa da manyan lambatu, na janyo toshewarsu a lokacin damuna da kuma haddasa ambaliyar ruwa.

Wakilin BBC Thomas Naadi ya kai ziyara wasu unguwanni da ke birnin Accra, ya gano yadda irin wannan tarin bola ta yi toroko a yankin da mutane ke hada-hada a kuma gefen bolar akwai masu saida abinci.

Wanda hakan ke barazana ga lafiyar mutane, kamar yadda jami'an lafiya suka bayyana.

Gwamnatin baya dai ta yi kokarin magance matsalar ta hanyar tsaftace muhalli a kowacce ranar asabar din karhen wata.

Labarai masu alaka