An bude babban taron majalisar koli a China

Babban zauren taron majalisar koli a China
Image caption China ita ce wadda tafi kowacce kasa yawan sojoji a duniya, kuma a shekaran baya-bayan nan ta na ta kawo sauye-sauyen zamanantar da rundunar sojin na ta

A yau ne Majalisar Koli ta Al'ummar China ta gudanar da babban taronta na shekara-shekara, inda ake sa ran za ta amince da yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwasrima.

Daga cikin sauye-sauyen da za a amince da su dai har da soke wa'√°din mulkin shugaban kasa, lamarin da zai bai wa Shugaba Xi Jinping damar ci gaba da zama a kan karaga har sai abin da hali ya yi.

Tuni dai wannan mataki da wani kwamitin majalisar ya kawo shawarar dauka ya fara shan suka, musamman daga kasashen Yamma, wadanda ke fatan China za ata ci gaba da sauye-sauye a tsarin siyasarta.

Sai dai wasu masana al'amuran da suka shafi China sun ce ba yadda za a yi China ta yi kama da kasashen Yamma ko da ta kwaikwaye su a wasu bangarorin. Jam'iyyar kwamunisanci a China ta bude babban taron ta a birnin Beijing na kasar.

Tuni firaminista Li Keqiang ya fitar da jadawalin matakan bunkasa tattalin arziki da gwamnati ke son shinfidawa a wannan shekara da kuma aka fara ganin sauyi.

Tattalin arzikin China ya bunkasa da kusan kashi 7 cikin 100 daga ranar daya ga watan junairun shekarar nan kawo yanzu, inda ko a bara ma hakan ce ta kasance a lokaci irin wannan.

Mista Li ya shaidawa babban taron gwamnati na yunkurin ganin ta wadata kasa daga arzikin Kwal da karafan da ta ke fiddawa suwa kasashen ketare.

Ya kara da cewa za a karawa hukumar tsaron kasa sama da kashi 8 cikin 100 a kasafin kudi, yawan kudin ya kai Yuwan tiriliyan uku.

Labarai masu alaka