Syria: Fararen hula na tsaka mai wuya a garin Ghouta

Luguden wuta a gabashin garin Ghouta
Bayanan hoto,

Sama da fararen hula 600 aka hallaka a gabashin garin Ghouta

Amurka ta fitar da wata sanarwa da ta yi Allawadai kan matakin luguden wuta da gwamnatin Syria ta yi a yankin da yan tawaye suka makale dake gabashin garin Ghouta.

Ta kira matakin na rashin imani, kuma hare-hare ta sama da Rasha babban kawar shugaba Bashrul Assad ta hallaka fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Sai dai shugaba Assad ya ce za a ci gaba da luguden wutar, ya kuma yi watsi da bayanan da masu kai agaji suka fada, inda yace karya ce tsagwaronta.

Wakilin BBC ya ce wannan ne karon farko da shugaba Assad ya yi bayani irin hakan, tun bayan fara luguden wutar da dakarun kasar da taimakon kawayenta suka yi na karbe iko da gabashin garin Ghouta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla fararen hula 600 aka hallaka a dan tsakanin nan, kuma mata da kananan yara ne suka fi shan wahala.

Yakin basasar Syria dai ya wuce shekara ta 4, tun bayan fara juyin juya halin da ya fada yankin gabas ta tsakiya.

A bangare guda shugaba Bassharul Assad, ya sha alwashin babu gudu ba ja da baya a yakin da 'yan tawayen da Amurka da kasashen yamma ke marawa baya.