Saudia: ''Babu wani haraji da muka kara wa masu ibada''

Masu ibada na gudanar da sa'ayi
Image caption A duk shekara musulmai daga sassa daban-daban na duniya na gudanar da aikin Hajji

Ma'aikatar Aikin Hajji da Umara ta kasar Saudiyya ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce a yi watsi da wata jita-jita da ake wallafawa a shafukan sada zumunta kan cewa gwamnati za ta sanya wasu kudade na daban ga masu aikin hajji da umara da suka shigo daga kasashen ketare.

Jaridar Almadina, wadda ake wallafawa da harshen Larabci, ta dauki labarin a ranar Litinin, inda ta yanko wani bangaren jita-jitar da aka wallafa ashafukan sada zumunta, kan cewa gwamnati za ta karbi Riyal 400 zuwa 700 ga duk wanda ya shigo kasar don yin ibada da shekarunsa suka wuce 18.

Kuma wai ma'aikatar aikin hajji da umarar za ta kafa wasu cibiyoyi a filayen jiragen kasar da cikin birnin Makka don karbar kudaden a hannu mutanen.

Gwamnatin ta tabbatar da babu wannan batun sam, amma ta na shirin sake fadada girman wuraren da Alhazai za su zauna wanda a halin da ake ciki wuraren sun yi kadan saboda an yi su ne don mutum miliyan takwas zuwa miliyan 15 kamar yadda tsarin shekarar 2020 ya tanada.

Amma yanzu za a fadada shi zuwa na mutum miliyan 30, ana kuma sa ran za a yi aikin ne daga yanzu zuwa shekarar 2030.

Labarai masu alaka