Saudiyya ta kare kanta kan yakin Yemen

Saudiyya ce ke matsayin jagorar kasashen musulmai a duniya
Image caption Ana ganin sarki Salman ya karawa dan shi yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman karfin fada aji da ya ke jagorantar tattaunawar manyan batutuwa da suka shafi kasar da yankin larabawa

Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al Jubeir ya kare matakin da kasarsa ta dauka na shiga yakin Yemen, inda ya ce 'yan tawaye ne suka haddasawa kasar halin da ta ke ciki a yanzu.

Da yake tattaunawa da BBC al-Jubeir ya zargi 'yan shi'a na kabilar Houthi a Yemen, da tilastawa yara 'yan shekara 9 shiga yakin da suke yi da gwamnati, da kuma sace kayan agajin da ake kai wa faraen hula.

Jami'an MDD sun ce ana dora alhakin mutuwar yawancin fararen hular da ake hallakawa a yakin kan Saudiyya da ke jagorantar kai hare-hare ta sama.

Da yake jawabi gabannin kai wata ziyara kasar Bahrain, da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman zai kai, Mista Jubeir ya ce gwamnatin Saudiyya na kokarin ganin an magance matsalar masu tayar da kayar baya, da 'yan tawaye da kusan daukacin kasashen Labarawa ke fama da su a halin yanzu.

Saudiyya dai ta na shan suka kan matakin shiga yakin da ake yi a Yemen, inda masu sharhi kan al'amuran gabas ta tsakiya ke ganin kamata ya yi ta zama mai shiga tsakani a duk lokacin da rikici ya barke a yankin kasashen labaran.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Ali Abdallah Saleh, kasar Yemen ta shiga tashin hankalin da ya faro kamar na siyasa inda daga bisani ya rikide na kabilanci.

Dubban fararen hula ne suka rasa muhallansu, yayin da wasu suka rasa rayukansu a shekarun da aka dauka ana yakin a Yemen.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan halin da fararen hular ke ciki, inda ta ce mata da kananan yara da tsofaffi ne suka fi shan wahala a kasar.

Labarai masu alaka