Kaduna: 'Za mu hukunta masu haddasa rikici'

Gwamna Nasiru El-Rufa'I
Image caption Kudancin jihar Kaduna na fama da rikicin addini da kabilanci

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria, ta alwashin za ta sanya kafar wando daya da masu haddasa tashin hankali a wasu yankunan jihar musamman Kudanci.

Gwamnati ta yi wannan kalami ne makwanni biyu bayan hatsaniyar da ta tashi a Garin Magani a karamar hukumar Kajuru, inda aka kona gidajen mutane da hallaka wasu da dama.

Ba wannan ne karon farko da ake samun rikici mai nasaba da addini da kabilanci a jihar Kaduna ba, kuma gwamnati ta sha shan alwashin magance matsalar.

Amma har yanzu ba ta sauya zane ba. Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya zargi wasu 'yan siyasar yankin da rura wutar rikicin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Labarai masu alaka