Amurka na zargin Koriya ta Arewa da kisan Jong-nam

Kim Jong-nam
Image caption Tun bayan mutuwar Kim jong-nam ake zargin dan uwansa Kim Jong-un da hannu a kisan shi

Amurka ta sake kakabawa Koriya ta Arewa karin takunkumi, bayan ma'aikatar cikin gida ta tabbatar da cewa gwamnatin Koriya ta Arewa ta yi amfani da wata guba wajen hallaka dan uwan shugaba Kim Jong-un.

A watan fabrairun bara ne dai wasu mata biyu suka aka kai wa Kim Jong-nam hari a filin jiragen sama na Malaysia, inda suka goge masa fuska da wata riga.

Wakiliyar BBC ta ce Jong-nam wani baudadden mutum ne, kuma dan uba ga shugaba Kim, sannan a baya ya sha sukar lamirin gidan su kan mulkin mulaka'un da suke yi a Koriya ta Arewa.

Inda ya kan fito bainar jama'a ya nuna rashin jin dadi akan wani mataki da dan uwansa ya dauka ko tafiyar da mulkin da ya ke zargin na zalunci ne.

A shekarar da ta gaba bayan mutuwarsa, ba a sake jin duriyar matasa da Dan shi daya tilo ba. Sai daga bisani dan ya wallafa wani hoton bidiyo a shafin internet inda ya jaddada shi da mahaifiyarsa su na cikin koshin lafiya.

Sai dai bai bayyana daga inda ya dauki bidiyon ba, ko kuma kasar da suke. A cewarsa rayuwarsu na cikin hadari, idan har dan uwan mahaifinsa ya san inda suke.

Koriya ta Kudu dai ta yi tayin a bata dama dan gano inda aka dauki bidiyon, daga bisani labarin ya bi shanun sarki.

Ma'aikatar ta ce matakin amfani da makami mai guba a bayyanar jama'a ya nuna yadda Koriya ta Arewa ba ta daukar dan adam da daraja ba.

Labarai masu alaka