Syria: Dubban fararen hula sun tsere daga garuruwansu

Jimillar mutanen da ke wadannan garuruwan sun kai dubu hamsin Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jimillar mutanen da ke wadannan garuruwan sun kai dubu hamsin

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta samu rahotannin da ke cewa wani kazamin fada a wani waje da 'yan tawaye su ka yi wa kawanya kusa da Damascus ya sa fararen hula a wasu kauyuka uku tserewa daga garuruwansu.

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniyar ya ce garuruwan sun hada da Hammouriyeh, Mesraba da kuma Mudeira.

Rahotanni sun nuna cewa jimillar mutanen da ke wadannan garuruwan dubu hamsin ne, kuma yanzu a na tunanin sun shige cikin yankin da 'yan tawayen ke iko domin neman mafaka.

A yanzu dai, dakarun Syria na ci gaba da shiga gabashin Ghouta inda su ke fafatawa da 'yan tawayen da aka alakanta da kungiyar Al-Qaeda.

Dubban fararen hula na cikin matsanancin hali yayin da yakin ke ci gaba da ruruwa, kuma da yawa sun rasa rayukansu.

Syria: Fararen hula na tsaka mai wuya a garin Ghouta

An zargi Koriya Ta Arewa da bai wa Syria makamai masu guba

Labarai masu alaka