An yi zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a Benin Republic

An zabi Shugaba Patrice Talon a shekarar 2016 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An zabi Shugaba Patrice Talon a shekarar 2016

'Yan sanda a Kwatano, a jamhuriyar Benin sun yi amfani da ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa wata zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati.

Wasu masu zanga-zangar sun cinna wuta a jikin shingaye da aka yi da tayoyi.

Dubban mutane ne su ka fito zanga-zangar wacce jam'iyyun adawa su ka shirya domin nuna hamayyarsu ga manufofin Shugaba Patrice Talon.

An zabi shugaban, wanda tsohon dan kasuwa ne a shekarar 2016, bisa alkawurran farfado da tattalin arzikin kasar. Sai dai shirinsa na sabunta manufofin cinikayya ya fuskanci adawa daga jama'ar kasar.

Dokar Nigeria ta durkusar da kasuwar motoci a Jamhuriyar Benin

An hana sallah a kan titi a jamhuriyyar Benin

Labarai masu alaka