Turkey: An bayar da belin 'yan jarida biyu

A na zargin ma'aikatan jaridar Cumhuriyet da goya wa kungiyoyin ta'addanci baya Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A na zargin ma'aikatan jaridar Cumhuriyet da goya wa kungiyoyin ta'addanci baya

Wata kotu a Turkiyya ta bayar da belin wasu 'yan jarida biyu wadanda su kai aiki da jaridar adawa kuma wadanda a ka tsare sama da shekara guda.

A na zargin Babban editan Jaridar Cumhuriyet, Murat Sabuncu da wakilin jaridar Ahmet Sik da wasu abokan aikinsu da goya wa kungiyoyin ta'addanci baya.

'Yan jaridar dai sun musanta zargin. Haka kuma a na tsare da shugaban kamfanin da ke buga jaridar Akin Atalay kusan kwanaki dari biyar.

Kungiyar Reporters Without Borders da ke fatutikar kare 'yan jarida a duniya ta yi Allah-wadai da shari'ar kuma ta yi kira da a yi watsi da zargin.

Turkey ta nemi goyon bayan NATO

Turkey: Erdogan zai iya mulki har 2029

Labarai masu alaka