Bai kamata a juya wa 'yan cirani baya ba - Fafaroma

Fafaroma Francis
Image caption Ko a lokacin bikin Kirsimati da ta wuce, Fafaroman ya yi kiran kar a manta da halin da 'yan gudun hijira su ke ciki a kasashen da yaki ya daidaita da 'yan ciranin da tlast ta sanya suka bar muhallansu

Fafaroma Francis ya soki kasashen duniya da suka maida hankali kan baki 'yan cirani, mako guda gabannin babban zabe a kasar Italiya.

A wani taron tunawa da kafa wata kungiyar tabbatar da zaman lafiya da kuma ta tallafawa 'yan gudun hijira da yawanci suka fito daga kasar Syria, Fafaroman yace duniya na nunawa mutanen da suka fito daga wasu kasashe, musamman ta banbancin matsayi misali talakawa tsana da tsangwama alhalin su ma ba sa jin dadin yadda suke.

Fafaroma Francis ya ce akwai kasashen da suka tsorata matuka da 'yan cirani, da hakan ya sanya suka sauya muradunsu.

Fafaroman bai ware kasa daya tilo a matsayin wadda ta fi nuna tsangwama ga 'yan cirani ko 'yan gudun hijira ba, illa ya yi abin nan na kan mai tsautsayi ga duk kasashen.

Yayin da Italiya za ta jinin jikinta saboda yadda gangamin yakin neman zabe ya gudana, da 'yan takara suka mayar da hankali kan baki 'yan cirani da gudun hijira.

Labarai masu alaka