'Iran na takura wa ma'aikatan BBC da iyalansu'

Ma'aikatan BBC
Image caption Fiye da ma'aikatan BBC na harshen Persa 20, aka turawa barazanar za a hallaka su

BBC ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da cin zarafin da ake yi wa ma'aikatanta na harshen Persa da ke birnin London da kuma iyalansu da ke can kasarsu ta Iran.

BBC ta yi korafin gwamnatin Iran ta fara wani gangamin razanarwa, da tsorata iyalan ma'aikatanta, har ta kai da ana kama wasu daga cikin 'yan uwansu da haramta musu yin balaguro.

Iran dai ta fara takurawa ma'aikatan BBC da ilansu tun bayan zaben shekarar 2009, a lokacin da ta zargi kasashen waje masu karfin fada aji da dagula lissafi a lokacin zaben.

A baya gwamnatin Iran ta haramtawa Iraniyawa ma'aikatan BBC da ke kasashen waje shiga kasarsu, da haramta musu mallaka wata dukiya da suke da ita a kasar.

Ciki har da dukiyar da suka gada daga iyayensu, sannan jami'an tsaro na yawan tuhumar iyalai kan laifukan kama karya da ba a tabbatar da su ba.

Za dai a gabatar da wannan koke ne gaban zauren hukumar kare hakkin bil'adam ta Majalisar Dinkin Duniya a Geneva.

Tsoron Za a kama su

A watan Oktobar shekarar da ta wuce, ma'aikatan BBC da suka halarci zaman makokin rasuwar mahaifin abokin aikinsu da ya rasu a kasar Iran. Ya shaida musu cewa an kira shi ta wayar tarho cewa mahaifinsa ba shi da lafiya.

A ka'ida kamata ya yi ya shirya tafiya gida dan gano halin da mahaifinsa ke ciki.

Amma ina, hakan ba mai yiwuwa ne ba saboda duk wani ma'aikacin BBC da ya fito daga kasar Iran na tsoron komawa gida saboda kar gwamnati ta sanya a cafke su, abun da ya iya yi shi ne amfani da kafar sadarwa ta Skype dan ganin halin da mahaifinsa ke ciki da kuma 'yan uwansa.

Mako guda bayan hakan, mahaifinsa ya rasu. Amma babu damar halartar jana'iza da zaman makoki, hasali ma mutanen da suka san shi ba su yi karanbanin zuwa don zaman makokin ba saboda tsoron abin da ka je ya zo.

Wannan dalili ne ya sanya ya zauna a birnin London, inda abokan aiki suka dinga zuwa can don yi masa ta'aziyya, wannan halin ya kara jefa su cikin tashin hankali.

Hatta kudi da sukan turawa iyaye ko 'yan uwa an haramta musu yin hakan, wannan halin suke ciki sama da shekara bakwai.

Labarai masu alaka