Iniesta ya koma atisaye bayan da ya yi jinya

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga

'Yan wasan Barcelona sun koma atisaye a ranar Litinin, bayan da kungiyar ta bayar da hutu a ranar Lahadi domin shirin fuskantar Chelsea.

Kafin 'yan wasan su fara komai sai da suka yi wa Lionel Messi tafi sakamakon haihuwa na uku da matarsa ta yi, an kuma sakawa yaron suna Ciro Messi.

Cikin manyan 'yan kwallon Barca da suka yi atisayen har da Andres Iniesta wanda ke murmurewa daga jinya da ya yi a rauni da ya ji a karawa da Atletico Madrid

Haka kuma matasan Barcelona biyar da suka hada da Carles Alena da Jose Antonio Martinez da Samu Araujo da Vitinho da kuma Marcus McGuane sun yi atisaye tare da manyan kungiyar.

Barca za ta karbi bakuncin Chelsea a wasa na biyu a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai a ranar Laraba, bayan da suka tashi 1-1 a karawar farko a Stamford Bridge a ranar 20 ga watan Fabrairu.

Labarai masu alaka