Julius Maada ya yi nasara a zagayen farko na zaben Saliyo

Nan da mako biyu za a gudanar da zagaye na biyu na zaben Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Julius Maada Bio ne ya lashe kashi 43 cikin 100 na zagayen farko na zaben

Shugaban 'yan adawa Julius Maada Bio ya lashe kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka yi a Saliyo.

Mista Maada Bio, ya lashe kashi 43 cikin 100 na kuri'un da aka kada, inda ya yi nasara akan abokin takararsa Samura Kamara na jam'iyyar All Peoples Congress da kashi daya rak.

Ya taba jagorantar Saliyo a lokacin mulkin soja a shekarar 1996.

Nan da makwanni biyu masu zuwa mutanen biyu za su sake karawa a zagaye na biyu na zaben.

Shugaba Ernest Bai Koroma dai zai sauka daga mukamin shugaban Saliyo, bayan shafe shekara 10 ya na kan karagar mulki.

Masu sanya ido kan zaben sun tabbatar da an yi shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba a kuma tada wata kura ba.

Ya yin da 'yan takara da mabiyansu, suka bada hadin kai wajen tabbatar da an yi zaben cikin tsari.

A shekarun 1990 kasar Saliyo ta fuskanci yakin basasar da ya girgiza kasar ta kowacce fuska.

Labarai masu alaka