'Na fadi gaskiya don a daina kallon mu barayi'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Jawabin Shehu Sani kan yawan albashin 'yan majalisa

Dan Majalisar dattawan Najeriya wanda ya fallasa yawan kudin da 'yan majalisu ke karba a duk wata, Sanata Shehu Sani, ya yi Karin haske kan dalilan da suka sa ya fallasa kudin da sanatocin ke karba a duk wata.

Sanatan ya ce bai yi wannan tonon silili ba da manufar tozarta zauren majalisar illa dai saboda kallon da wasu ke yi musu na barayi marasa gaskiya masu boye abun da suke samu.

Ya kara da cewa sama da shekara 19 kenan da ake zargin 'yan majalisa na karbar miliyoyin nairori, amma kuma sun kasa fitowa su kare kansu., su kuma yi wa 'yan Najeriya bayanin ainahin kudaden da suke dauka a matsayin albashi ko na alawus-alawus.

Sannan ya ce ya yi maganar ne don sauran bangarorin gwamnati kama daga alkalai, da ministoci da gwamnoni da duk wadanda suke rike da madafun iko su bayyanawa 'yan kasa adadin kudin da suke samu da kuma abin da suke yi da su.

Wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai ya tambayi Shehu Sani ko zai dawo da miliyoyin kudin da ya karba na kusan shekara uku da ya yi a matsayin da ya ke kai?

Sai ya kada baki ya ce: ''Ba wai shekara uku da ya yi a matsayin Sanata ba ake magana, abun lura shi ne sama da shekara 19 kenan ana kan wannan turbar, kuma daruruwan mutane sun yi aikin majalisar sun tafi, wasu kuma za su zo.''

Ya kara da cewa ''Saboda haka ko ma a wanne lokaci ka fadi gaskiya, ka dai fade ta, kuma abin da ya sa mutane suke gudun fadar gaskiya shi ne gudun abin da zai same su.''

Image caption Sanata Shehu Sani ya ce ya san ba lallai ne maganar da ya yi ta yi wa wasu dadi ba, to amma ya fada ne dan a daina yi wa 'yan majalisa kallon barayi

Labarai masu alaka