Bolivia: An hana yara ziyartar 'yan uwa a gidan kaso

Gidan kason Palmasola
Image caption Fursunonin sun taba yi wa Fafaroma Francis korafin rashin kyawun wurin da ake tsare da su, a lokacin da ya taba kai ziyara a shekaru uku da suka gabata

Akalla fusrsunoni 7 aka a hallaka a kasar Bolivia, a lokacin da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka shiga dan raba dandazon masu zanga-zanga a gidan kason.

Sama da mutane 20 ne suka jikkata ciki har da 'yan sanda. Akallah 'yan sandan kwantar da tarzoma 2000 ne suka shiga gidan kason Palmasola da ke gabashin birnin Santa Cruz dan tabbatar da doka da oda.

Hukumomi sun ce wasu gungun fursunoni dauke da muggan makama suka tada hatsaniyar amma daga bisani an ci lagonsu.

Kusan kwanaki 10 da suka gabata ne dai aka fara zanga-zangar, bayan gwamnatin Bolivia ta haramtawa yara 'yan kasa da shekara 6 ziyartar iyaye ko 'yan uwansu da ke gidan kaso.

A shekarar 2015 fafaroma Francis ya kai ziyara gidan kason Palmasola, inda fursunoni suka yi korafin su na cikin mummunan yanayi a gidan da kuma rashin kula da su.

Labarai masu alaka