Ma'aikaciyar jirgin da ta fado daga jirgin sama ta mutu

Jirgin Kamfanin Emirates Hakkin mallakar hoto Getty Images

BBC ta samu labarin cewa ma'aikaciyar jirgin Emirates wadda ta fado daga jirgin a ranar Laraba ta rasu.

Wani mai magana da yawun kamfanin ya ce, matar, wadda ba a bayyana asalin kasarta ba, an kai ta wani asibiti da gaggawa da ke yankin Kisubi wanda ke da nisan kilomita 16 daga inda ta fadi, amma ta rasu jim kadan da isar su asibitin.

Rahotanni sun ce ma'aikaciyar jirgin ta fado ne a yayin da jirgin ke shirin kwasar fasinjoji don tafiya.

Hukomar zirga-zirgan jiragen sama ta Uganda ta ce sun kaddamar da bincike.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, wai ma'aikaciyar jirgin ta bude kofar fitar gaggawar kuma cikin rashin sa'a sai ta fada kasa, inda jirgin yake tsaye.

Mai magana da yawun Asibitin Kisubi Edward Zabonna, ya shaidawa BBC cewa ma'aikaciyar "ta samu raunuka a baki dayan fuskarta da gwiwowinta."

Ya ce ta fita daga hayyacin ta amma tana da rai lokacin da aka isa da ita asibiti a ranar Laraba, sai dai ba ta jima ba ta rasu.

Kamfafin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wata sanarwa daga Kamfanin jirage na Emirates cewa: "Wata ma'aikaciyarmu ta fado daga wata kofa da ke bude yayin da fasinjoji ke shirin shiga."

Kamfanin jirgin saman na birnin Dubai ya yi alkawarin cewa zai bayar da "cikakken hadin kai" don gudanar da bincike kan abun da ya afku.

Labarai masu alaka