An kaddamar da ATM na sayen magani a Afrika ta kudu

ATM Pharmacy Hakkin mallakar hoto Reuters

An kaddamar da wata na'ura mai kama da ta diban kudi a banki ta ATM, wadda ita kuma ke bayar da kwayoyin magani.

Na'urar wadda jama'a suka yi mata lakabi da ATM Pharmacy, tana bai wa mutanen da likita ya rubutawa magani daga asibiti.

Sannan na'urar an samar da ita ne domin cututtuka masu tsanani kamar, tarin fuka da da ciwon suga da cuta mai karya garkuwar jiki, AIDS ko SIDA.

Na'urar ita ce irinta ta farko a Afirka, da aka fara kafa wa a garin Alexandra da ke Johannesburg.

Kuma tun kaddamar da na'urar ake samun cunkoso a asibitoci.

Na'urar tana fitar da magunguna ne maimakon kudi, sannan akwai tarho a jikinta.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mai bukatar magani zai yi magana da jami'in bayar magani ta tarho.

Mutane za su iya kiran kwararrun masu bayar da magani domin neman shawara.

Marassa lafiya a wasu asibitocin a Afirka ta Kudu su kan bi layi su jira sama da sa'a 12 domin karbar magani.

Amma idan layi ya kai ga mutum, cikin minti uku na'urar za ta ba shi maganin da ya bukata.

An shafe lokaci mai tsawo ana gwada na'urar kafin soma amfani da ita.

Wannan dai wani sabon ci gaban fasaha ne aka samu a fannin kiwon lafiya a duniya.