An kashe sojojin Isra'ila a West Bank

Al'amarin ya faru ne a yammacin kogin Jordan kusa da garin Jenin Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption Al'amarin ya faru ne a yammacin kogin Jordan kusa da garin Jenin

Rundunar sojan Isra'ila ta ce an kashe wasu sojojinta biyu a wani hari na da gan-gan, inda maharin ya kutsa motar da ya ke ciki da karfi.

Al'amarin ya faru ne a yammacin kogin Jordan kusa da garin Jenin.

An tsare direban motar wanda dan asalin Falasdinu ne. A farkon watan nan ne wasu dakarun tsaron iyakar Isra'ila da sojoji biyu su ka raunata a wasu hare-hare guda biyu na kutsen mota a arewacin Isra'ila.

Daruruwan 'yan Falasdinu ne su ka yi zanga-zanga ranar Juma'a domin cika kwanaki dari tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana birnin kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Labarai masu alaka