An harbe wasu masunta a Tafkin Cadi

Harin dai ya faru ne a tsibirin Tudun Umbrella a tafkin Cadi, wanda ke da iyaka da Najeriya, da Cadi da Kamaru Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Harin dai ya faru ne a tsibirin Tudun Umbrella a tafkin Cadi, wanda ke da iyaka da Najeriya, da Cadi da Kamaru

Wasu da a ke zargin mayakan boko haram ne sun harbe wasu masunta guda biyar a wani tsibiri a arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban kungiyar masunta na jihar Barno, Abubakar Gamandi ya ce an kashe mutanen ne saboda su na taimakawa sojoji wajen cigiyar daliban makarantar Dapchi da 'yan boko Haram din suka sace a watan jiya.

Har yanzu dai ba a gano daliban ba.

Harin dai ya faru ne a tsibirin Tudun Umbrella a tafkin Cadi, wanda ke da iyaka da Najeriya, da Cadi da Kamaru.

Labarai masu alaka