Ana zaben shugaban kasa a Rasha

Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a 1999, Vladimir Putin ke shugabanci a Rasha

An bude runfunar zaben shugaban kasa a Rasha, inda shugaba Vladimir Putin ke neman wa'adin shugabanci na hudu.

Tun a ranar Asabar aka soma zaben a gabashin Rasha, sa'a tara tsakani kafin a fara zaben a Moscow.

Shugaba Putin da ke neman sake wasu shekaru shida kan mulki, na fafatawa ne da 'yan takara guda bakwai a zaben.

Bayan ya jefa kuri'arsa, a Moscow, Mista Putin ya ce yana ganin nasara a sakamakon da zai ba shi "hakkin gudanar da aikin shugaban kasa."

Daga cikin masu hamayya da Putin a zaben, sun hada da attajirin Rasha Pavel Grudenin da kuma dan kishin kasa Vladimir Zhirinovsky.

An haramta wa babban mai adawa da gwamnatin Rasha, Alexei Navalny, shiga zaben.

Mista Navalny ya yi kira ga magoya bayan shi su kauracewa zaben.

Tun a 1999, Vladimir Putin mai shekaru 65, ke shugabanci a Rasha, ko dai a matsayin shugaban kasa ko kuma Firaminista.

Rahotanni sun ce a wasu yankuna, ana janyo ra'ayin mutane su fito su kada kuri'a ta hanyar ba su abinci kyauta ko kuma da rahusa a gidajen cin abinci da ke yankunan.

Kamfanin dillacin labaran kasar na Interfax ya ruwaito cewa mutane sun fito sosai domin kada kuri'a a gabashin kasar.

Wannan zaben shi ne na farko da aka taba gudanar wa a Crimea tun lokacin da yankin ya dawo ikon Rasha daga Ukraine.

Zaben na zuwa a daidai lokaci n da ake cika shekaru hudu da shugaba Putin ya kaddamar da yankin Crimea a matsayin ikon Rasha, matakin da Ukraine da kasashen yammaci ke ci gaba da adawa da shi.

Labarai masu alaka