'Yan taxi za su dauki tsofaffi kyauta a Afrika ta kudu

Afrika ta kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An fi amfani da bus a matsayin taxi a Afrika ta kudu

Wasu 'Yan taxi a Afrika ta kudu sun sanar da matakin daukar mutanen da suka haura shekaru 70 a kyauta.

Wani dan taxi da mai suna Yassen Abrahams ne ya fara sanar da daukar matakin a shafinsa na facebook.

Daga baya kuma abokan aikinsa su ma suka amince su dauki masu manyan shekarun kyauta a Bonteheuwel.

Abharams mai shekaru 25 ya sha yabo a shafukan sada zumunta na intanet musamman a garin Bonteheuwel, da ke kusa da Cape Town.

Ya ce daga karfe Tara na safe, duk fasinjan da ya haura shekaru 70, za a dauke shi ne a kyauta.

Daga karfe 10 kuma a ranakun karshen mako.

Abhrams ya ce ya lura da wadanda suka yi ritaya da kyar suke iya biyan kudin taxi, domin ya sha daukarsu a kyauta.

Sannan a cewarsa: "A kullum zauna-gari-banza na tilasta muna mu ba su kudi ko kuma mu dauke su a kyauta, wannan ya sa wani tunani ya zo min cewa, me ya sa ba za mu dauki tsofaffi a kyauta ba? Yawancinsu ba su da lafiya kuma ba su iya tafiya."

Ya ce mutuwar mahaifiyarsa a 2016 ta girgiza shi, kuma daga lokacin ne ya fara lura da yanayin tsofaffi, inda yawancinsu ba su da kudin shiga taxi.

Bayan samun goyon baya a garinsa yanzu Mista Abraham yana kira ga 'yan taxi a fadin kasar su taimakawa mabukata a cikin al'umma.

Labarai masu alaka