Damben Audu Argungu da Sojan Kyallu
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Damben Audu Argungu da Sojan Kyallu

Dambe sama da 13 aka fafata a safiyar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Mohammed Abdu ne ya hada wannan rahoton

Cikin karawar an yi kisa a wasa bakwai ciki har wasan da Audu Argungun daga Arewa ya buge Sojan Kyallu daga Guramada a turmin farko, sauran damban babu kisa wato canjaras aka tashi.

Wasannin da aka yi kisa:

 • Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu ya buge Bahagon Dan Jibga daga Arewa.
 • Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu ya doke Shagon Bahagon Maru daga Arewa.
 • Shagon Bahagon Gurgu daga Kudu ya doke Shagon Dan Aminu daga Arewa.
 • Dan Yalo daga Arewa ya yi nasara a kan Shagon Bahagon Kanawa daga Kudu.
 • Gudumar Dan Jamilu daga Arewa ya buge Dogon Aleka daga Kudu.
 • Bahagon Sisco daga Kudu ya doke Dan Aliyu Langa-Langa daga Arewa.

Dambatawar da aka yi canjaras kuwa:

 • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Bahagon Dogon Aleka daga Kudu.
 • Nasiru Shagon Bahagon Gurgu daga Kudu da Shagon Aminu daga Arewa.
 • Bahagon Roget daga Arewa da Bahagon Jafaru daga Kudu.
 • Shagon Kunnari daga Kudu da Shagon Shagon Alhazai daga Arewa.
 • Dan Yalow Autan Sikido daga Kudu da Bahagon Alin Tarara daga Arewa.
 • Dogon Bahagon Sisco daga Kudu da Autan Dan Bunza daga Arewa.
 • Shagon Dogon Kyallu Guramada da Bahagon Dan Shago daga Arewa.

Labarai masu alaka