Najeriya: Me ya sa Buhari ya fasa zuwa Rwanda?

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Najeriya za ta yi nazari kafin amincewa da yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fasa zuwa Rwanda domin halartar wani taron shugabannin Tarayyar Afrika kan yarjejeniyar kasuwanci.

Shugaban zai halarci taron ne kan batun yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya da za a gudanar ranar Talata kafin sanar da fasa zuwansa.

A cikin sanarwar da ta fitar, ma'aikatar harakokin wajen Najeriya ta ce an soke tafiyar shugaban ne don samun isasshen lokacin da za a yi nazari mai zurfi game da yarjejeniyar da kasashen Afrika suka amince a kafa a watan Janairun 2012.

Yarjejeniyar ta shafi gudanar da kasuwanci kyauta ba haraji tsakanin kasashen da suka sanya hannu.

A ranar Larabar da ta gabata ne majalisar zartawa ta amince Najeriya ta shiga yarjejeniyar.

Wannan ne ya sa shugaba Buhari zai tafi Rwanda domin sanya hannu.

Wasu masu sharhi na ganin, an amince Najeriya ta shiga kawancen ba tare da diba ribar da kasar za ta samu ba idan har ta shiga.

Tuni dai wasu jami'an gwamnati suka isa Kigali, yayin da wasu rahotanni a Najeriya suka ce an bukaci su dawo bayan Buhari ya fasa tafiya taron.

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta yi gargadi game da amincewa da yarjejeniyar, inda ta ce matakin zai gurgunta masana'antu tare da haifar da rasa guraben ayyukan yi ga 'yan kasa.

Yanzu dai ba a san matsayin Najeriya ba a yarjejeniyar, mai karfin tattalin arziki a Afrika.