Puigdemont: Kataloniya za ta amince da kwarya-kwaryar 'yanci

Mr Puigdemont ya tsere Belgium bayan da Catalonia ta ayyana 'yancin kai a wata Oktobar bara Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mr Puigdemont ya tsere Belgium bayan da Catalonia ta ayyana 'yancin kai a wata Oktobar bara

Shugaban awaren Catalonia, Carles Puigdemont ya ce Kataloniya za ta iya yadda da irin tsarin mulkin kasar Switzerland na kwarya-kwaryar 'yanci a maimakon cikakken 'yanci daga Spaniya.

Mr Puigdemont, wanda ya tsere Belgium bayan da Kataloniya ta ayyana 'yancin kai a wata Oktobar bara ya ce ya na bakin ciki da cewar za a daure shi a gidan kaso idan ya fadi ra'ayinsa a Spaniya.

Dubban 'yan Kataloniya sun yi wata zanga-zanga a birnin Barcelona domin nuna tsananin adawarsu ga neman 'yancin kan.

Tsohon Firam ministan Faransa wanda kuma haifaffen Kataloniya ne, ya ce ba a yi nasara ba a shirin neman 'yancin kan, a yayin da Turai da gwamnatin Spaniya da al'ummar Kataloniya ke nuna adawa ga shirin.

Labarai masu alaka