Dapchi: Sojin Najeriya sun yi fatali da zargin Amnesty

Makarantar sakandaren Dapchi
Image caption Mako hudu kenan da sace 'yan matan sama da 100 amma har yanzu ba amo ba labarinsu

Rundunar sojin Najeriya ta zargi kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty International da son raba kan 'yan kasar da kuma sanyaya gwiwar mutanen da ke kokarin taimakon rundunar don shawo kan matsalar tsaro a kasar.

Sojin na mayar da martamni ne kan zargin da Amnesty ta yi musu cewa sojojin sun yi biris da gargadin cewa 'yan Boko Haram za su kai hari sa'o'i kalilan gabannin a sace 'yan matan sakandaren Dapchi sama da 100.

Sanarwar da sojin suka fitar ta ce "Muna so mu kawar da shakku daga zukatan mutane cewa babu wata rundunar tsaro da aka shaida wa satar 'yan matan Dapchi gabanin faruwar hakan, kamar yadda Amnesty ke ikirari."

Ta kara da cewa Amnesty, "wacce ba ta son ci gaban Najeriya" na kokarin sa rundunar ta yi "bakin jini wajen 'yan Najeriya da idon duniya.

A lokacin da ya ziyarci garin na Dapchi a makon da ya gabata, Shugaba Muhammadu Buhari, ya shaida wa iyayen yaran cewa sakacin jami'an tsaro ne ya kai ga afuwar lamarin.

Sannan ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa wurin kubutar da su.

Rahoton na Amnesty na zuwa ne wata guda bayan da wadanda ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka sace 'yan matan a lokacin da suke makaranta a garin Dapchi.

A tata sanarwar, Amnesty ta kara da cewa yawancin shugabannin al'umar yankin, sun sanar da sojoji tun lokacin da suka samu labarin jerin gwanon motocin maharan na wani kauye mai nisan kilomita 30 daga garin na Dapchi, kwana guda gabannin sace 'yan matan.

Sun yi ikirarin cewa ko a lokacin da maharan suka iso an sanar da sojojin, amma ba su yi wani abu a kai ba.

Tun da farko mai magana da yawun sojin Najeriya ya ce tuni gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai yi kwakkwaran bincike kan gazawar jami'an tsaro a yankin da ta kai ga sace matan.

Kawo yanzu iyayen 'yan makarantar na zaman zullumi da tashin hankalin rashin sanin ainahin inda 'ya'yansu suke.

Shugaba Buhari ya ce satar yaran wani "babban bala'i ne" sannan ya nemi afuwar iyayen matan kan abin da ya faru.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce, ta tura karin dakarun tsaro da jiragen yakin domin nemo 'yan mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ce ta sace su.

Image caption Gwamnati ta ce tana kokarin kubutar da 'yan matan

Satar dalibai 110 ta haifar da yanayi iri-iri ga rayuwar jama'ar garin da ma na jihar baki daya.

Kungiyar Boko Haram wacce ake zargi da kai hari a makarantar, ba ta ce komai ba kawo yanzu.

Sama da shekara Hudu kenan da sace 'yan matan sakandaren Chibok sama da 200 da Boko Haram ta yi, gwamnatin Najeriyar ta kubutar da wasu daga ciki ta hanyar amfani da tattaunawa tsakaninta da mayakan.

Sai dai har yanzu akwai sama da 100 a hannn kungiyar ta Boko Haram.