Jami'an Rasha na shirin ficewa daga Birtaniya

Sergei Skripal da 'yarsa Yulia
Image caption An zargi Rasha da hannu a harin gubar Nerve da aka kaiwa tsohon jami'in hukumar leken asiri mai cin tudu biyu

Jami'an diplomasiyyar Rasha 23 sun gama tattara kayansu dan barin birnin London a yau talata, bayan gwamnatin Birtaniya ta dibar musu wa'adin ficewa daga kasar.

Hakan ya biyo bayan tsamin da dangantaka ta yi tsakanin kasashen biyu, kan zargin Rasha na da hannu a harin gubar Nerve da aka kai wa tsohon jami'in leken asirin Rasha da Birtaniya Sergei Skripal da 'yarsa Yulia a birnin Salisbusry.

A ranar asabar ita ma rashar ta sanar da jami'an diplomasiyyar Birtaniya su fice mata daga kasa.

Firaiminista Theresa May za ta gana da manyan jami'an hukumar tsaron Birtaniya dan sake tattaunawa kan matakin da ya kamata su dauka nan gaba.

Rundunar 'yan sandan Birtaniya masu yaki da ta'addanci ta ce an yi kokarin kashe wani tsohon dan leken asirin Rasha da 'yarsa a birnin Salisbury da wata guba.

Sergei da Yulia Skripal na asibiti cikin matsanancin rashin lafiya tun bayan da a ka tsince su a sume a kan wani benci ranar Lahadi,

Rahotanni sun nuna cewa da alama an sa ma Sergei da Yulia Skripal gubar ne da gangan.

Labarai masu alaka