Ana tilastawa 'yan matan Rohingya karuwanci

'Yan gudun hijirar Rohingya
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce mata da kananan yara da tsofaffi, su ne suka fi kowa shan wahala a lokutan tashin hankali irin wannan

Wani bincike da BBC ta gudanar, ya gano ana safarar yara mata 'yan kabilar Rohingya da suka haura shekara 10 dan yi karuwanci a sansanin 'yan gudun hijira da ke Bangladesh.

Baki 'yan kasar waje da suke sha'awar yin jima'i da yara na samun damar daukar irin wadannan mata cikin sauki, wadanda suka baro jihar Rakhine ta Myanmar saboda tashin hankali.

Wata yarinya mai suna Awara yar shekara 14 da suka tsere daga Myanmar, aka kuma hallaka iyayenta a iyakar kasashen biyu ta dade ta na neman mai tallafa mata.

Ta ce halin da ta samu kanta a ciki, na gararanba a gefen titi, ya sanya da wasu mata a cikin mota suka bukaci taimaka ma ta ta bi su ba tare da tunanin wani abu makamancin hakan zai faru ba.

Anwara ta kara da cewa ''Bayan sun dauke ni, sai suka min alkawarin za su taimaka min na samu ingantacciyar rayuwa. Amma maimakon hakan sai suka kai ni birnin Cox's Bazar''.

''Ba da jimawa ba sai suka kawo min wasu maza biyu. Tare da tsorata ni da wuka kan cewa idan ban amince da bin da suke bukata ba za su kashe ni. Daga nan sai suka mintsine ni da saman wukar a ciki na, suka kuma lakada min duka saboda na ki yadda su haike min,'' inji Anwara.

A baya-bayan nan dai ana ta samun korafin safarar 'yan mata daga sansanonin 'yan gudun hijira da suke zaune a Bangladesh, kuma ana daukar su ne dan yin karuwanci.

Mata da 'yan mata, da kuma tsofaffi na cike da fargabar halin da za su samu kansu a ciki a duk lokacin da aka samu matsala irin hakan a matsugunan da suke zaune.

Labarai masu alaka