Boko Haram ta sako 'yan matan sakandaren Dapchi

Wasu dalibai a aj su na daukar karatu
Image caption Sama da makwanni hudu kenan da sace 'yan matan a lokacin da suke makarantar kwana a garin Dapchi na jihar Yobe

Iyayen 'yan matan Dapchi 110 da mayakan Boko Haram suka sace sun ce an sako 'ya'yan nasu.

Sai dai ba dukkansu aka sako ba.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da sako 'yan matan na Dapchi.

Mahaifin daya daga cikin 'yan matan, Kundili Bukar, ya gaya wa BBC cewa da sanyin safiyar Laraba ne wasu mutane da ake tsammani 'yan Boko Haram ne suka mayar da matan garin a motoci.

A cewarsa, sun ajiye su ne kawai suka tafi kuma 'yan matan sun nuna alamar matukar gajiya.

Kundili Bukar ya kara da cewa iyaye na ta rububin zuwa domin dubawa da kuma dauko 'ya'yansu.

Daya daga cikin iyayen 'yan matan ya shaida wa BBC cewa kungiyar Boko Haram ta rike daya daga cikin 'yan matan sannan biyu sun mutu.

Sai dai Kwamishinan 'yan sandan jihar Yobe, Abdulmaliki Sunmonu, bai tabbatar da komawar matan gida ba, ko da yake ya ce shi ma ya ji labarin sakinsu.

A watan jiya aka sace matan, lamarin da ya janyo mummunar suka kan gwamnati da jami'an tsaron Najeriya.

A wancan lokacin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sace 'yan matan a matsayin wani bala'i da ya shafi kasar baki daya.

Dapchi na cike da murna

Mazauna garin na Dapchi sun shaida wa BBC cewa Boko Haram ta dawo da akasarin matan da ta sace daga garin a watan jiya.

Biyu daga cikin iyayen yaran sun fada wa BBC cewa an kai matan garin ne a cikin motoci hudu inda aka ajiye su a kofar garin na Dapchi su kuma suka nufi gidajen iyayensu. An yi ta murna da ganinsu.

Manuga Lawal, wacce 'yarsa Aisha ke cikin matan da aka sako, ya ce ya yi magana da ita ta wayar tarho kuma yanzu haka yana kan hanyarsa ta komawa Dapchi domin su yi ido biyu da ita.

Ya kara da cewa yana matukar murnar dawowarta gida, inda ya yi wa Allah godiya.

Ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu ne mayakan Boko Haram suka sace 'yan matan bayan sun kai hari a garin na Dapchi.

Da farko gwamnatin jihar Yobe ta ce dukkan 'yan matan sun tsira. Sai dai daga bisani ta tabbatar da sace su, inda ta nemi afuwa daga wurin iyayen matan bisa kuskuren da ta yi.

Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta ce sace 'yan matan tamkar wani alhaki ne da ya fada wa gwamnatin APC mai mulki saboda yadda ta rika caccakar PDP din lokacin da aka sace 'yan matan makarantar Chibok a 2014.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka