Shekara guda da kai harin gadar London

'Yan uwan mamatan na ajiye furanni a wurin da akai kai harin
Image caption Maharin ya bi ta kan mutanen da ke tafiya akan gadar da mota, daga bisani 'yan sanda suka harshe shi

A ranar Alhamis ne za a fara addu'ar cika shekara guda ga wadanda suka mutu ko jikkata a harin ta'addancin da aka kai gadar Westminsters da ke birnin London shekarar da ta wuce.

Mutane 5 ne suka rasu ciki har da dan sanda daya. 'Yan majalisa za su yi shiru na minti guda, duk dai a wani bangare na tunawa da mamatan.

A shekarar da ta gabata ne matashi Khaled Masood (Mas'oud)ya afka kan mutanen da ke tafiya da kafa akan gada.

Daga bisani kuma ya sauka ya na sukar mutane da wukar da ke hannunsa yayin da 'yan sanda suka bude masa wuta ya mutu nan ta ke.

A watan Yuli ma wasu mahara uku sun hallaka mutane 7 da jikkata wasu da dama a kusa da gadar birnin London.

Har wa yau a dai wannan watan, wani mahari da ya afkawa mutanen da ke salla a wajen wani masallaci kuma mutum guda ya rasu.

Labarai masu alaka