An fara zaben shugaban kasa a Masar

Abdul Fattah al-Sisi (L) and his sole challenger Moussa Mustafa Moussa Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Abdul Fattah al-Sisi (Hagu) da dan takara Moussa Mustafa Moussa

An bude rumfunan zabe a Masar, kuma shugaba mai ci Abdel Fatah al-Sisi tare da wani mutum guda ne kawai za su tsaya takara.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun soki tsarin zaben saboda rashin kwararan 'yan takara.

Wasu 'yan takarar kuma sun koka da yadda suka ce ana amfani da jami'an tsaro wajen tursasa musu da su janye daga takarar.

Motocin safa-safa dauke da amsa-kuwwa na ta yawo a birnin Al Kahira suna rera wakokin da ke kira ga 'yan kasar Masar su fito su kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar.

Za dai a dauki kwanaki uku ana gudanar da zaben, kuma ana sa ran cewa shugaba mai ci, Abdel Fattah El-Sisi ne zai lashe zaben babu wata hamayyar a zo a gani.

Mousa Mostafa Mousa shi ne mutum guda tilo da yake takara tare da shugaba al Sisi kuma a 'yan kwanakin baya ya rika ikirarin cewa yana goyon bayan shugaban kasar.

'Yan takara masu yawa dai sun janye daga tsayawa a wannan zaben, bayan da suka yi kukan ana muzguna musu, yayin da wani dan takarar guda ke fuskantar tuhuma ta shari'a cewa yana takara babu izini, bayan da 'yan sanda suka kama shi.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Allon talla na shugaba Abdel Fatah al-Sisi

Amma ofishin kamfen din shugaba El-Sisi ya musanta cewa an hana wasu 'yan takarar tsayawa a wannan zaben. Amma 'yan adawa sun rika kira ga magoya bayansu da su kauracewa zaben kwata-kwata.

Sa'o'i kadan kafin a fara zaben, rahotanni sun ruwaito cewa jami'an tsaron kasar sun kashe wasu 'yan tawaye shida da ake tuhuma da kai wani harin bam na ranar Asabar a birnin Iskandiriyya.

Rahotanni sun ce an kai harin ne a cikin wani yunkuri na kashe wani babban jami'in tsaro a nan.

Labarai masu alaka