Zimbabwe: Ana tuhumar Grace Mugabe da fasa-kwauri

Ana tuhumar Grace Mugabe da fasakwauri Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Grace Mugabe da maigidanta Robert Mugabe a lokacin suna kan mulki

'Yan sanda a Zimbabwe sun tabbatar da cewa matar tsohon shugaba Mugabe, Grace na da hannu a fasa-kwaurin hauren giwa daga Zimbabwe.

Hukumar da ke kula da albarkatun dazukan kasar na tuhumar Misis Mugabe da laifin fitar da hauren giwan da darajarsu ta kai miliyoyin dalolin Amurka

An dai rika fitar da haramtattun kayan ne zuwa kasashen China da Hadaddiyar Daular Larabawa da Amurka.

Misis Mugaben ba ta ce uffan ba game da wannan batun.

Kakakin jami'an 'yan sanda ya fada wa jaridar Sunday Mail ta Zimbabwe cewa tuni aka fara gudanar da bincike a kan Grace Mugabe.

Shugaban hukumar da ke kula da albarkatun dazuzzukan kasar ya ce an kira shi ta wayar tarho daga fadar shugaban kasa a bara, inda aka umarce shi da ya bayar da takardun izini saboda a fitar da hauren giwa zuwa China.

Wani mai daukar hotunan namun daji, Adrian Steirn, ya ce yana da hujjojin da suka tabbatar cewa masu fasa-kwaurin hauren giwa na da alaka da matar tsohon shugaban kasar Mugabe.

Ya ce ya shafe watanni yana gudanar da nasa binciken a boye a cikin kasar ta Zimbabwe.

A bara ma Misis Mugaben ta fuskanci matakin shari'a a Afirka ta Kudu bayan da wata mata mai tallata kayan sawa ta shigar da kara cewa Misis Mugaben ta raunata ta da waya a goshinta.

Labarai masu alaka