An sayar da dukkan tikitin kallon Madrid da Juventus

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real ce za ta fara ziyartar Juventus a Gasar Zakarun Turai

A safiyar Litinin aka kammala sayar da tikitin kallon wasan da za a yi tsakanin Real Madrid da Juventus a Santiago Bernabeu.

Real Madrid wadda ke rike da Kofin Zakarun Turai, za ta karbi bakuncin Juventus a wasa na biyu na daf da na kusa da na karshe a ranar 11 ga watan Afirilu.

Ba wannan ne karon farko da aka sayar da dukkan tikitin kallon tamaula ba, illa yadda aka saye shi da wuri.

Jaridar Marca ta ce magoya bayan Juventus 4,000 ne za su halarci Bernabeu mai cin 'yan kallo 80,000, inda za su zauna daga bangaren Arewacin Fili.

Sai dai kuma Real ce za ta fara jiyartar Juventus a ranar 3 ga watan Afirilu a Italiya.

Real Madrid da Juventus sun fafata sau 19 a tsakaninsu, inda Real ta ci fafatawa tara, Juventus ta yi nasara a wasa takwas, sannan suka yi canjaras a karo biyu.

Labarai masu alaka