Buhari ya kaddamar da majalisar wadatar da abinci

Muhammadu Buhari Nigeria's Presient

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar da majalisar shirin samar da yalwataccen abinci mai gina jiki, wadda shi da kansa zai shugabanta.

Mambobin majalisar sun hada da gwamnonin jihohin Kebbi da Taraba da Filato da Legas da Ebonyi da Delta.

Akwai kuma wakilan ministoci da ma'aikatun gwamnati masu ruwa da tsaki a lamarin.

Sai dai da babu wakilan manoma da makiyaya a majalisar.

Gwamnatin tarayyar ta ce wadannan bangarori biyu suna da damar da za su mika bayanan damuwarsu da shawarwarinsu ga majalisar.

Sabuwar majalisar za ta kula da batutuwan da suka jibanci wadata Najeriya da abinci ne.

Labarai masu alaka