Za a bunkasa kiwon zuma a Nigeria

Kudan zuma
Image caption Bincike ya gano yawancin kudan zumar kasashen Turai sun gudo kasashen Afirka, kuma kashi 48 cikin 100 suna Niajeriya

Masu kiwon zuma a Najeriya sun gudanar da wani taro a Legas, babban birnin kasuwancin kasar wanda zai share fagen wani taron masu ruwa da tsaki kan kiwon zumar na nahiyar Afirka da za a yi a Abuja a watan Satumba.

Taron ya duba sabbin hanyoyi kiwon zuma, da hanyoyin da za a bunkasa shi dan fitarwa zuwa kasashen ketare.

Daya daga cikin manufar taron ita ce yaki da masu sayar da zumar da a ka yi wa algus.

Malam Ya'u Sarkin Baki, shi ne shugaban kungiyar ma su kiwon zuma a arewa maso yammacin Najeriya, kuma ya ce babbar matsalar da suke fuskanta a kiwon zuma shi ne rashin kayan aiki.

Sannan kuma akwai rashin shigar gwamnati cikin lamarin don bunkasa shi ta hanyar samar da wadatattun kayan aikin da suke bukata.

''Wata matsalar da muke fuskanta ita ce ta masu sayar da baragurbin zuma, hanyar da za mu magance matsalar ita ce ta bai wa mutane horo a kuma ba su kayan aikin ya kuma kasance a kowa ce jiha ta Najeriya muna da manoman zuma 1,000 ta hakan ne za mu magance matsalar,'' in ji Malam Ya'u.

Ya kara da cewa: ''Wani abu da zai bayar da mamaki shi ne kudan zumar da ake da su a kasashen Turai sun gudu, kuma kasashen Afirka suka kwararo. Bincike ya nuna kusan kashi 48 cikin 100 suna Najeriya, to ka ga idan ba a dauki matakin kara fadada noman ba don ya bunkasa to babu wata riba da za a samu a ciki.''

Labarai masu alaka