An kalubalanci matasan Ghana kan noman zamani

Gonar shinkafa
Image caption Malam Bukar ya ce da gwamnatin kasar Ghana za ta bai wa matasa tallafin noman shinkafa kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yi, za a samu alkahiranda za su ja hankalin matasan kan noman zamani

A kasar Ghana masana harkar noma sun kwadaitawa matasa rungumar noman rani da ake samun alkhairi mai tarin yawa a cikinsa.

Duk da ya ke noman tsohowar sana`a ce da magidanta ke amfani da ita wurin ciyar da iyali da samun kudaden shiga, hakan bai sa matasan zamani rungumar ta ba.

Mafi yawan matasa sun yi watsi da harkokin noma saboda kallon da suke yi mata na tsohon yayi, amma wasu masana na cewa akwai sirrin samun kudaden shiga.

Mallam Bukar Tijjani shi ne mataimakin shugaban hukumar abinci da harkokin noma na Majalisar Dinkin Duniya, a hira da ya yi da wakilinmu na Ghana Muhammad Fahd irin dabarun harkar noman zamani da ya kamata matasa su runguma.

Sai dai wani matashi Zakariya Adam Alafas da BBC ta zanta da shi, ya yi korafin rashin tallafin gwamnati kan harkar noman dalilin da ya sanya matasa ke baro kauyuka da dawowa birane don samun sana'o'in da suke ganin za su kawo musu kudaden shiga.

Ya yin da Shamsudden Muhammad Futua ya ce raggon taka ce ke sanyawa matasa ba sa sanya kan su a ayyukan da suka shafi noma, inda ya kara da cewa a wannan zamani matasa su na son budar ido su ga sun yi kudi cikin sauki ba tare da shan wata wahala ba.

Labarai masu alaka