Malala ta isa gida Pakistan

Malala da mahaifinta da kuma 'yan uwanta
Image caption Shekaru shida ta suka gabata, Malala na gdon asibiti a Birtaniya

A karon farko cikin shekara 6, matashiya Malala YousafZai da ta dauki lambar zaman lafiya ta Nobel ta isa kasar ta wato Pakistan.

Shekara 6 da ta gabata ne mayakan kungiyar Taliban suka harbi Malala a Ka da kawayenta a gundumar Swat Valley a lokacin da suke kan hanyar zuwa makaranta.

Malala mai shekara 20, ta samu gurbin karatu a jami'ar Oxford ta Birtaniya, kasar da ta ke zaune tare da iyayenta da kannenta.

Malala za ta halarci wani taro a kasarta, sannan su gana da firai minista Shahid Khaqan Abbasi.

A shekarar 2012 ta bar kasar Pakista cikin hlin rai kwa-kwai mutu-kwakwai, a lokacin reshen kungiyar Tehriki Taliban na Pakistan ne suka dauki alhakin kai harin.

Sun kuma tabbatar da Malala suka kai wa harin saboda nuna adawa da manufar Taliban, da karfafawa 'ya'ya mata gwiwar yin karatu.

Wakiliyar BBC ta ce Malala Yousefzai ta dawo inda ya kasance mahaifarta, tun a watan Oktobar 2012 ne ta shiga Birtaniya a matsayin mara lafiya da aka har ba a kai.

Bayan daukar lokaci a asibiti, ta kamallama karatun sakandare, a yanzu ta samu gurbin karatu a jami'ar Oxford ta Birtaniya, ta na kuma halartar taruka da dama a duniya da ta ke karfafa ilimin 'ya'ya mata.

Labarai masu alaka