Najeriya: Shugabannin al'umma za su taka rawa a zabe mai zuwa

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje
Bayanan hoto,

Jihar Kano na daga cikin jihohin da ke kawo yawan kuri'u a arewacin Najeriya

Wata kungiyar fafutukar tabbatar da kyakkyawan shugabanci da ci gaban jihar Kano ta fara gangamin yadda zaben shugabanni zai kasance a jihar a zaben shekarar 2019.

Kungiyar Kano LEADS a arewacin Najeriya ta ce in har ana so jihar ta bunkasa to sai an sauya tsarin da ake bi wajen zabo shugabannin al'umma.

Daga cikin masu wannan yunkuri dai akwai wadanda ke ganin ba a damawa da su yadda ya kamata a tsarin shugabanci a matakai daban-daban.

Farfesa Nazifi Darma na cikin wadanda suka kafa kungiyar, ya kuma shaida wa BBC cewa lokaci ya yi da ya kamata shugabannin al'umma kama daga masu unguwanni da dagatai da matasa su hadu don zabar wakilan da za su ciyar da al'umma gaba.

Farfesa Darma ya ce: ''Duk wanda yake son tsayawa takara, sai ya gabatar da kansa ga wadannan wakilan al'umma, a zauna don tattaunawa kan irin ayyukan da mazauna yankin suke bukatar dan takara ya yi musu idan sun mara masa baya ya ci zabe.''

Ya kara da cewa lokaci ya yi da jama'a za su daina turawa 'yan siyasa mota suna bade su da kura.

''Ba kai tsaye za a yi abun ba, za a yi komai a rubuce da kuma shaidu saboda guje wa rashin cika alkawari da wasu 'yan siyasa ke yi da zarar sun samu biyan bukata,'' in ji Farfesa Darma.

Saura kasa da wata 11 a gudanar da manyan zabukan shekara ta 2019 a Najeriya, amma tuni jama'a daban-daban a kasar suka fara daura damarar ganin sun kai ga biyan bukatunsu na shugabanci.