MDD ta kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiya a Liberia

Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD
Image caption Akwai zarge-zargen dakaraun na MDD sun ci zarafin mata ta hanyar lalata da su

Bayan shafe shekara goma sha biyar ta na aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar Liberia, Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen wannan aiki.

Tsahon wannan lokacin kasar ta samu gagarumin ci gaba musamman na kawo karshen yakin basasa da dorewar zaman lafiya.

Akalla jami'an Majalisar Dinkin Duniya dubu goma sha shida, da suka fito daga kasashe sama da goma ne suka gudanar da wannan aiki da aka fi sani da UNMIL.

An yi kiyasin kusan farar hula dubu dari biyar aka hallaka a lokacin yakin basasar kasar tsakanin shekarar 1989 zuwa 2003, sannan kusan rabin al'umar kasar ne suka rasa muhallansu.

Wasu rahotanni kuma sun ce kusan kashi tamanin cikin dari na mata da yaran Liberia sun fuskanci wani nau'in cin zarafi ciki har da lalata da su a lokacin yakin.

Kuma bayan kawo karshen yakin, Liberia ta yi nasarar gudanar da zabukan shugaban kasa har sau uku.

Zabe na baya-bayan nan da aka yi a watan Oktoba ya kafa tarihi, inda tsohon zakaran kwallon kafa George Weah ya nasara bayan an tafi zagaye na biyu na zaben.

Labarai masu alaka