'Ko shugaba Buhari bai isa hanani fadar gaskiya ba'

Dino a wakar hip-hop
Image caption Dan minsitan man Najeriya, Uche Kachikwu ya ce ba domin matsayin babansa ne Dino Melaye ya fito a bidiyonsa ba.

Dan majalisar dattawan Najeriya mai jawo ce-ce-ku-ce, Sanata Dino Melaye ya ce ba zai yi shiru da bakinsa ba matukar ya ga wani abu da ake gudanarwa a gwamnati da bai dace ba.

Ana yi wa Sanata Dino Melaye kallon yana cikin mutanen da suka buwaya sakamakon yawan shiga takaddama, ana kuma jibanta shi da wani rukuni na `yan majalisa da ke hana-ruwa-gudu ga bangaren zartarwa.

Dan majalisar dattawan ya yi kaurin-suna wajen arangama da gwamnoni daban-daban a jihar Kogi, ciki har da gwamna mai ci.

Ya shaidawa BBC cewa baya tsoron tsage gaskiya a duk inda ta kama a fade ta, ba kuma ya duba daga jam'iyyar da mutum ya fito indai batun gaskiyar ya kama ko dan PDP, ko APC mai mulki.

''Ni ba na tsoron kowa, idan akai abin da ba daidai ba kuma na ga babu gaskiya a ciki sai na fada, ba na jin tsoron kowa indai ina da gaskiya. A halin da ake ciki ni fa ko shugaban kasa Muhammadu Buhari, ko Bukola Saraki, ko Dogara kai ko uban da ya haife ni idan ya yi ba daidai ba sai na fada, babu wanda ya isa ya hanani fadar gaskiya sai dai a kashe ni,'' inji Dino Melaye.

Kan batun rashin jituwar da ba ya yi da gwamnan jiharsa Yahya Bello, ya ce babu wani abu da ya taba faruwa tsakaninsu. Sannan dama can ya saba kalubalantar tsofaffin gwamnonin PDP na jihar da suka gabata, kuma ba zai koma jihar Kogi ba har sai shekara mai zuwa ba kuma zai ce uffan kan batun sa da gwamna Bello ba saboda su na gaban kotu.

Senata Dino ya yi suna wajen rayuwar bushasha da facaka da kudi, inda a kwanakin baya ya fito cikin wata waka an nuna shi cikin motar alfarma ana ta watsa daloli sama.

Dino ya kare kan sa da cewa ba satar kudin wani ko gwamnati ya yi dan sayan motoci da rayuwar kasauta da ya ke yi ba, saboda daman can shi mutum ne mai son motoci da rayuwar jin dadi.

Ya kara da cewa ''Babu wanda ya isa ya hanani jin dadi, dan babu wani hadisi ko annabi da ya ce kar mutum ya ji dadin rayuwarsa. Ba kudin wani na sata ba bare ace ban yi daidai ba, sannan ni mutum ne mai son wake-wake kwanan nan ma zan fitar da sabbin wakokin da na yi.''

Ko da yake ana yawan kalubalantar a matsayinsa na wakilin al'uma bai kamata ya dinga haka ba, amma ya ce ya na yi wa al'umarsa aiki ko a yanzu shi kadai ne a cikin Sanatoci da ya mallaki gidan marayu.

Labarai masu alaka