Ana kidayar kuri'un zabe a karo na biyu a Saliyo

Sierra Leone election Runoff Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ana can ana ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasar Saliyo a zagaye na biyu da aka gudanar.

An dai nuna damuwa dangane da rashin fitowar masu kada kuri'a sosai idan aka kwatanta da yadda aka gani a zagaye na farko.

Dan takarar jam'iyyar adawa wanda a baya ya jagoranci juyin mulki Julius Maada Bio na fafatawa ne da Samura Kamara na jam'iyya mai mulki.

Sai cikin mako mai zuwa ne ake sa ran samun cikakken sakamakon zaben bayan hukumar zaben kasar ta kammala tattara alkaluman masu kada kuri'a.

Shugaban kasa mai barin gado Ernest Bai Koroma wanda ya kammala wa'adin mulkinsa karo na biyu.

Shi ne ya zabi Mista Kamara domin ya gaje shi idan ya lashe zaben a karkashin jam'iyya mai mulki ta All People's Congress (APC).

Shi kuma Julius Mada Bio wanda shi ne jagoran jam'iyyar adawa ta Sierra Leone People's Party (SLPP).

Ya sha kaye a hannun shugaba Koroma a zaben shugaban kasa da aka gudanar shekaru biyar da suka gabata.

Mista Mada Bio ya taba mulkin kasar a shekarar 1996, inda ya mulki kasar na wasu watanni bayan ya yi wani juyin mulki.

Labarai masu alaka