Damben boksin: Anthony Joshua ya doke Joseph Parker

Asalin hoton, LAWRENCE LUSTIG
Zakaran boksin ajin masu nauyi Anthony Joshua
Zakaran boksin ajin masu nauyi Anthony Joshua ya lashe kambun WBO, bayan da dukkan alkalan wasan damben suka ba shi nasara kan abokin karawarsa Joseph Parker dan asalin kasar New Zwealand.
Sun yi ta gumurzu da abokin karawar nasa har na tsawon turmi na goma sha biyu babu kisa a wasan da aka yi daren Asabar a filin wasa na Principality Stadium da ke birnin Cardiff na kasar Wales.
Anthony Joshua ne ke rike da kambun bokisin na WBA da WBO da IBO da kuma na IBF, kuma hakan dai na nufin cewa Anthonin ya yi nasarar hada manyan kambun damben boksin uku wuri guda kenan.
Tun da fari an tabbatar wa Anthony Joshua dalar Amurka miliyan 20 idan ya yi nasara.
Shi kuma Joseph Parker ya tashi da fam miliyan 13 duk da cewa ya sha kaye.
Asalin hoton, Reuters
Anthony Joshua da Joseph Parker a lokacin karawarsu
Kimanin mutane 80,000 ne suka shiga filin wasan domin kallon wannan damben, kuma an nuna wasan a kasashe 215 kai tsaye.
Kafin wannan karawar, babu wani dan dambe da ya taba doke Anthony Joshua a dukkan karawar da yayi guda 20. Hasali ma ya doke dukkan abokan karawarsa da knockout.
Kuma a tarihi, babu dan wasan boksin da ya taba hada kambun boksin guda hudu na duniya a lokaci guda.
Ana sa ran Anthony Joshua zai kara da mai rike da kambun WBC, Deontay Wilder domin kafa tarihin hada dukkan kambunan a wuri guda.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti Daya Da BBC Na Rana 25/01/2021, Tsawon lokaci 1,05
Minti Daya Da BBC Na Rana 25/01/2021