'Dole mu saurari kasashen duniya' - Aung San Suu Kyi

Rohigya refugees Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan kabilar Rohingya Musulmi na gudun hijira a Myanmar

Shugabar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta fada wa kasarta cewa dole ne ta mayar da hankali kan abin da kasashen duniya ke fada mata idan ba ta son kimarta ta zube.

Shugabar ta sha suka saboda gazawarta na yin allawadai da matakan sojin kasar da suka tilastawa Musulmi 'yan Rohingya dake yammacin kasar su 700,000 su nemi mafaka a Bangladesh.

Suu Kyi ta na gargadin ne a wata tashar talabijin a yayin da ake bukin cika shekara biyu da darewarta kan karagar mulkin kasar, inda ta ce gwamnatinta ta koyi darussa masu yawa.

Ba ta bayyana irin darussan da gwamnatinta ta koya ba.

Ta tabo rikicin yankin Rakhine amma ba ta ce komi ba dangane da cin zarafin 'yan Rohingya da ke gudana a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matakan da sojin kasar ke dauka a matsayin na share kabilar Rohingya daga doron kasa.

Shugab Suu Kyi ta ce tana kokarin gina tafarkin zaman lafiya ne tsakanin bangarorin Musulmi da mabiya adinin Bhudda.

Labarai masu alaka